Bangladesh

An yi artabu tsakanin Jami’an tsaro da masu zanga-zanga a Bangladesh

'Yan sandan kasar Bangladesh sun cafke wasu daga cikin masu zanga-zanga a Dhaka.
'Yan sandan kasar Bangladesh sun cafke wasu daga cikin masu zanga-zanga a Dhaka. REUTERS/Andrew Biraj

A kasar Bangladesh, yanzu kura ta lafa bayan da aka share tsawon yinin Lahadi ana artabu tsakanin jami’an tsaro da magoya bayan ‘yan adawa, wadanda ke kokarin hana shirya zabukan kasar a ranar 5 ga watan gobe.

Talla

Rikicin ya kara tsananta ne bayan da dimbin magoya bayan ‘yan adawar da suka taru a wani dandali, suka sami labarin cewa ‘yan sanda sun hanawa shugabarsu Khaleda Zia damar halartar wani taron gangami a birnin Dhaka fadar gwamnatin kasar.

Zia, Tsohuwar Firimiya ce a kasar Bangladesh kuma ta shirya hada gangami ne domin neman Firaminista Sheikh Hasina ta yi murabus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.