Isa ga babban shafi
Lebanon

An soma shari'ar wadanda ake zargi da kashe Hariri na Lebanon

Tsohon Firaministan Lebanon Rafiq Hariri
Tsohon Firaministan Lebanon Rafiq Hariri
Zubin rubutu: Abdoulkarim Ibrahim
Minti 2

Su dai wadannan mutane 4 da ake zargi da hannu wajen kashe tsohon firaministan, ba daya daga cikinsu da aka kama, duk da cewa masu shigar da kara na danganta su da kungiyar nan mai gwagwarmaya da makamai a kasar wato Hizbullah da kuma gwamnatin Syria wajen bayar da umurnin aikata kisan.

Talla

Akwai dai wasu manyan jami’an gwamnatin ta Labanan da dama da suka tsallaka rijiya ta baya a irin wadannan hare-hare da suka je gaban kotun da ke birnin Hague domin bayar da shaida.

Mutanen da ake tuhuma dai su ne Mustafa Amine Baddredine, sai Salim Jamil Ayyash, da Husseini Hasan Onesi da kuma Assad Hasan Sabra, wadanda aka ce suna da alaka ko dai da gwamnatin Syria ko kuma da kungiyar Hizbullah.

Ko shakka babu dai kisan da aka yi wa tsohon firaministan ya yi matukar sauya al’amurra a fagen siyasar kasar ta Labanan, tare da kara fitowa fili da kiyayyar da ke akwai tsakanin ‘yan Sunni da ke marawa Hariri da kuma ‘yan Shi’a da ke kawance da Hizbullah ko kuma Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.