Palasdinu

Bankin IMF ya ce zaman lafiyan gabas ta tsakiya zai iya taimakon Palasdinu

Ginin cibiyar IMF
Ginin cibiyar IMF

Asusun bada lamunin Kudi na Majalisar dunkin Duniya ya fitar da bayannan da ke cewar samun zaman lafiyar yankin Gabas ta tsakiya ka iya habaka tattalin arzikin kasar Palasdinu, rashin zaman lafiyar kuma na iya sa kasar ta ci gaba da samun koma-baya.Asusun ya ce rashin zaman lafiya a yankin Gabas ta tsakiya na iya kara yawan Bashi ga kasar ta Palesdinu ke karba.An dai dade ana kokarin tattaunawa tsakanin Isra’ila da Palesdinu a wani shirin da kasar Amurka ta ce ita ke jagoranta.