Isa ga babban shafi
Lebanon

An kafa gwamnatin gamin gambiza a Lebanon

Priministan Lebanon Tammam Salam
Priministan Lebanon Tammam Salam REUTERS/Mohamed Azakir/Files
Zubin rubutu: Nasiruddeen Mohammed
Minti 1

Jiya Asabar Priministan Lebanon Tammam Salam ya kaddamar da gwamnatin gamin gambiza a kasar, lamarin daya kawo karshen kiki kakar siyasar da aka shafe watanni 10 ana yi, yayin da kuma yakin basasan Syria, da ke makwabta da ita ya dagule. Majalisar Ministocin mai membobi 24, ta kunshi ‘yan kungiyar Hesbullah ta ‘yan shi’a, da keda fada a ji a kasar, da kawayenta, da kuma bangaren tsohon Priminista Saad Hariri mabiya sunni, da ke goyon bayan ‘yan tawaye, a rikicin kasar Syria.A ‘yan watannin da suka gabata bama bamai sun yi ta tashi a Beirut, babban birnin kasar, da ma wasu sassan kasar ta Lebanon, da ke auna yankuna da ‘yan Hezbollah ke da karfi. 

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.