Isa ga babban shafi
India

An yanke wa wasu matasa hukuncin kisa saboda fyade a India

Wasu yara 'yan kasar Indiya, da ke zanga zangar neman a hukunta masu fyade
Wasu yara 'yan kasar Indiya, da ke zanga zangar neman a hukunta masu fyade REUTERS/Amit Dave/File
Zubin rubutu: Nasiruddeen Mohammed | Mahmud Lalo
Minti 1

A jiya laraba, wata kotu a kasar India, ta yankewa wasu matasa uku hukuncin kisa, bayan da aka same su da laifin yin garkuwa da wata mata ‘yar shekaru 19 tare da yi mata fyade.A dai bara ne India ta tsaurara hukuncin da ake yankewa masu aikata fyade tun bayan da wasu gugungu matasa suka afkawa wata daliba a kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar ta daga baya.Lamarin fyade na kokarin zama ruwan dare a kasar ta Indiya, inda mata ke cikin wani mummunan halin zama cikin fargaba. 

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.