Syria-Kuwait

Kungiyar Larabawa ta nemi warware rikicin Syria a siyasance

Taron kasashen Larabawa.
Taron kasashen Larabawa.

Shuwagabanin Kasashen Larabawa ta kawo karshen taronta a wannan talata a kasar Kuwaiti, inda bukaci a samo hanyar warware rikicin kasar Syriya a siyasance.

Talla

A cikin sanarwar da suka fitar mahalarta taron sun yi kiran neman mafitar wannan rikici a siyasance, karkashin kudirin da zaman taron Geneva na 1 wanda ya tanadi kafa gwamnatin rikon kwarya a kasar ta Syriya.

Zaman taron da ya hada mambobin kungiyar ta hadin kasashen Larabawa 22, ya bukaci samar da gwamnatin rikon kwaryar da za ta sake gina kasar ta Syria , tare da samar da fahimtar juna a kasar, ta hanyar mutunta ‘yanci da martaba Syria a matsayin kasa daya dunkulalliya

Wannan mataki da zaman taron na kungiyar ya dauka, ya dusar da fatan da ‘yan adawar kasar Syriya ke da shi wanda a jiya talata shugabansu Ahmad Jarba ya koka tare da neman mahalartansa da su matsawa kasashen duniya lamba domin ganin su taimakamawa mayakan ‘yan tawayen kasar da makamai masu karfi, wajen kawar da gwamnatin kasar

Sai dai kuma daga cikin mambobin kungiyar kasasashe ta Larabawa akwai kasashe irinsu Iraki da Aljeriya da suka nuna adawarsu karara da kifar da gwamnatin Bashar Al’assad

Rikicin kasar Siriya da ya balle a watan Maris 2011 sakamakon wani boren al’umma da ya rikide ya zama yakin basasa, kawo yanzu ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane dubu 146 a yayin da wasu miliyan 9 suka yi hijira, ko kuma kauracewa gidajensu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.