Syria-MDD

'Yan gudun hijirar Syria sun haura milyan daya a Libanan

'Yan gudun hijirar Syria a Siracusa
'Yan gudun hijirar Syria a Siracusa Reuters/Antonio Parrinello

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce yawan ‘yan gudun hijirar kasar Siriya da ke zaune a Lebanon ya zarta Miliyan daya a halin yanzu. Majalisar ta ce mafi yawa daga cikin ‘yan gudun hijirar na zaune ne a birni na biyu mafi girma a kasar ta Labanan wato Tripoli.

Talla

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar dunkin Duniya ta bayyana cewar akalla suna yi wa ‘yan gudun Hijirar 2,500 rijista a kowace rana wato akalla mutum 2 a kawane minti 1 kenan.

Majalisar ta kara da cewa rabin su kuwa yara kanana ne kuma dukkaninsu suna rayuwa ne cikin kunci da talauci da kuma yin dogaro akan kayan agaji dake shigowa kasar.

To sai dai kamar yadda rahoton na UNHCR ke cewa, kasar Labanan dake kula da wadannan ‘yan gudun hijrar na fama da dawainiyar da ke neman fin karfinta.

Saboda haka ne ma Hukumar ta bukaci kasashen duniya da su hanzarta wajen taimakawa kasar domin magance wannan matsalar domin kuwa a cewar majalisar, Labanan kadai ba za ta iya daukar wannan nauyin ba.

Wannan rikicin na Syria dai ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dubu dari da hamsin yayin da kusan rabin al’ummar kasar suka tsere suka bar gidajensu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.