Falasdinawa

Hamas da Fatah sun amince su hada kai

Manyan Wakilan Hamas da Fatah na Falasdinawa da tattauna yarjejeniyar kafa gwamnatin Hadaka
Manyan Wakilan Hamas da Fatah na Falasdinawa da tattauna yarjejeniyar kafa gwamnatin Hadaka REUTERS/Mohammed Salem

Shugabannin Falasdinawa, Hamas da Fatah da ke mulki a Zirin Gaza da gabar yamma da Kogin Jordan sun amince su kafa gwamnatin hadin kai nan da makwanni biyar kamar yadda wata majiya daga babbar kungiyar Falasdinawan ta tabbatar.

Talla

Bangarorin biyu sun cim ma yarjejeniyar ne a Gaza, kamar yadda Majiyar ta tabbatarwa Kamfanin Dillacin Labaran Faransa.

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da bangarorin biyu ke yunkurin kafa gwamnatin Hadaka, domin sun sha yin irin wannan yunkuri amma daga baya al’amarin ya roshe.

Sasantawa da Isra'ila.

Kasar Isra'ila ta ki amincewa da bukatar shugaban Falasdinawa, Mahmud Abbas na sanya sharudda kafin ci gaba da tattaunawar sulhu da ta ki ci ta ki cinyewa a tsakaninsu.

Shuagba Abbas yace zai ci gaba da tattaunawa da Israila ne kawai idan ta jingine gine-ginen a Yankunan Falasdinawa, abinda wani jami'in Israila yace ba za su amince da haka ba.

Matakin na zuwa ne a dai dai lokacin da Jakadan Amurka, Martin Indyk ke ganawa da wakilan bangarorin biyu dan shawo kan su koma teburin tattaunawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.