Falasdinawa

Abbas ya nada Firaministan Falesdinawa

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas
Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas Reuters/Mohamad Torokman

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas, ya nada Rami Hamdallah a matsayin sabon Firaminista da zai jagoranci gwamnatin hadaka, tsakanin Hamas da Fatah. Yayin da har yanzu an kasa cim ma jituwa a tsakanin bangarorin biyu dangane da wanda za a nada a matsayin Ministan harkokin waje.

Talla

Majiyoyi a birnin Ramallah da ke yankin yamma da kogin Jordan, sun tabbatar da cewa a yammacin jiya alhamis ne Mahmud Abbas ya aikewa hukumomin Gaza da wasikar da ke sanar da su cewa ya zabi Hamdallah a matsayin sabon Firaministan Falasdinu.

To sai dai majiyar ta ci gaba da cewa babban abin da ya hana sanar da sunayen mambobin sabuwar Majalisar Ministocin Falasdinu shi ne sabanin kan wanda za a nada a matsayin Ministan harkokin waje, mukamin da Abbas ke son a bai wa wani mai suna Riyad Al Malki wanda ya taba rike wannan mukami tun a shekara ta 2007.

Ita dai kungiyar Hamas wadda ke rike da yankin Gaza, ta bukaci a a bayar da wannan matsayi ne a hannun Ziad Abu Amr, wanda ya taba rike mukamin mataimakin Firaminista a yankin gabar yamma da kogin Jordan.

Tuni dai Amurka ta aike wa sabon Firaministan da goron gayyata zuwa birnin Washington, kuma akwai yiyuwar ya gana da shugaba Obama kafin ya gana da wasu ‘yan Majalisar dokokin Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI