Syria

Mata ‘yan gudun hijirar kasar Siriya na kokawa akan makomar Jariransu

nytimes.com

A yayin da ake shirye shiryen gudanar da zaben shugaban kasa a cikin kasar Siriya ‘yan mata da dama daga cikin ‘yan gudun hijira sun haifi ‘ya’ya a sansanonin sun a ‘yan gudun hijira a wasu kasashe

Talla

Wannan ne ma ya sa akasarin Matan da ke gudun hijira a kasar Lebanon ke kokawa akan makomar Jariran da suka Haifa a wata kasa dab a tasu ba, da kuma ke zaman yan gudun hijira su ma.

A wani labarin kuma akalla kashi 95 na ‘yan gudun hijirar kasar Siriya da ke kasashen waje, wadanda suka cancanci jefa kuri’a ne suka jefa kuri’arsu a zaben shugaban kasar da ake sa ran zai mai da shugaba Bashar al-Assad a kan karagar mulkin kasar.

Kwamitin hukumar zaben ta kasar Siriya ne ya fitar da wannan bayanin na cewar akalla kashi 95 na ‘yan kasar Siriya da ke gudun hijira a kasashen waje ne suka jefa Kuri’arsu a zaben shugaban kasar, da ake sa ran gudanarwa a farkon wannan Makon.

Bayanin dai ya nuna cewar ‘yan kasar ta Siriya da ke zaune a yankunan da Gwamnatin kasar ke kula da su za su jefa tasu kuri’a ne ranar Laraba Mako daya bayan da aka kammala na ‘yan gudun hijira a kassahen waje.

Shugaban hukumar zaben kasar ya ce a Ofisoshin jakadancin kasashe 43 na yankin Larabawa ne ‘yan Siriyar suka jefa tasu kuri’a.

Sai dai tun ba’a je ko’ina ba, ‘yan tawayen kasar Siriyan masu kokarin kawarda Gwamnatin kasar tare da samun taimakon kassahen Turai, sun kushewa zaben da suka hango basu da nasara a ciki.

A Jajibirin gudanar da zaben dai babbar Jaridar da ke goyon bayan gwamnatin kasar Al-Watan ta fidda Alkalumman cewar fiye da mutane Dubu 200 ne suka yi Rajista a Ofisoshin jakadancin kasashe 39.

Sai dai Kamfanin dillancin labarai na SANA ya buga labarin cewar ya zuwa ranar Assabar ta karshen Sati ba’a tantance da adadin mutanen da suka jefa kuri’a ba, amma za’a sanar da sakamakon ne bayan kammala zaben da za’a gudanar a nan cikin kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.