Syria

Ana zaben shugaban kasa a Syria

Wasu 'yan Syria na jefa kuri'unsu a birnin Beirut na Lebanon
Wasu 'yan Syria na jefa kuri'unsu a birnin Beirut na Lebanon REUTERS/Sharif Karim

A yau talata, mutane sama da milyan 15 ne ke jefa kuri’unsu domin zaben shugaban kasa a Syria, a daidai lokacin da kasar ke ci gaba da fama da yakin basasar da ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane.

Talla

Tuni dai aka buda rumfunan zabe domin bai wa jama’a damar jefa kuri’unsu a wannan zabe da ake ganin cewa ko shakka babu shugaba mai ci wato Bashar Al Assad shi ne zai yi nasara, ta la’akari da yanayin da kasar ke ciki a yau.

Akwai dai wasu ‘yan takara biyu da ke karawa da da Assad, wato Maher Al-hajjar wanda a halin yanzu yake rike da mukamin dan majalisa, da kuma wani hamshakin dan kasuwa mai suna Hassan Al Nouri.

Ma’aikatar cikin gidan kasar ta bayyana cewa an kafa rumfunan zaben fiye da dubu tara a sassa daban daban na kasar yayin da aka dauki matakan tsaro domin bai wa jama’a damar jefa kuri’unsu, to sai dai zai kasance abu mai wuya a iya gudanar da zaben a wasu yankuna inda yanzu haka dakarun gwamnati ke ci gaba da gwabza fada da ‘yan tawaye.

Jagoran ‘yan adawar kasar Ahmad Jarba, ya bukaci al’ummar kasar da su kasance a gidajensu, inda ya bayyana zaben na yau da cewa ba ya da amfani, domin kuwa mutum daya ne ya shirya shi kuma shi ne dan takarar wato Basahr Assad.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.