Isra'ila-Falesdinawa

Isra'ila ta soki Amurka game da goyon bayan gwamnatin Palasdinu

Shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas da Firaministan Isra'ila Benjamin Netenyahu
Shugaban Palasdinawa Mahmud Abbas da Firaministan Isra'ila Benjamin Netenyahu REUTERS/Mohamad Torokman/Sebastian Scheiner/Pool

Ministoci da dama a Isra’ila sun soki Amurka bayan da ta goyi bayan sabuwar gwamnatin hada-ka da aka kafa tsakanin Hamas da Fatah a Palasdinu.

Talla

Ministan yada labaran Isra’ila Gilad Erdan, ya ce abin da Amurka ta yi babban kuskure ne, domin kuwa ba ta yadda za a goyi bayan gwamnatin da ke kunshe da ‘yan Hamas wadanda a cewarsa su ne ke kashe ‘yayan Yahudawa.

A shekaranjiya ne dai Amurka ta bayyana cewa a shirye take domin yin aiki da gwamnatin da aka kafa a Palasdinu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.