Syria

Ana kidayar kuri'un da aka jefa a zaben shugabancin kasar Syria

Bashar Assad na jefa kuri'arsa a zaben shugabancin kasar
Bashar Assad na jefa kuri'arsa a zaben shugabancin kasar REUTERS/SANA/

Yanzu haka dai hukumar zaben kasar na ci gaba da tattara sakamakon kuri’ar da aka jefa a jiya talata, inda tun kafin ma a fitar da sakamakon magoya bayan Bashar Assad suka fara bukukuwan domin murnar cewa dan takarar nasu ya yi nasara.

Talla

A jiya talata ne dai mutane sama da milyan 15 suka jefa kuri’unsu domin zaben shugaban kasar ta Syria, a daidai lokacin da kasar ke ci gaba da fama da yakin basasar da ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane.

To sai dai tuni aka hakikance cewa Bashar Al Assad ne zai yi nasara a zaben, ta la’akari da yanayin da kasar ke ciki a halin yanzu.

Akwai dai wasu ‘yan takara biyu da ke karawa da da Assad, wato Maher Al-hajjar wanda ke rike da mukamin dan Majalisa, da kuma wani hamshakin dan kasuwa mai suna Hassan Al Nouri.

Tun a jajibirin zaben ne jagoran ‘yan adawar kasar Ahmad Jarba, ya bukaci al’umma da su kasance a gidajensu, inda ya bayyana zaben da cewa ba ya da amfani, domin kuwa mutum daya ne ya shirya shi kuma shi ne dan takarar wato Basahr Assad.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.