China

Shekaru 25 da murkushe tarzomar Tiananmen a kasar China

Dandalin Tiananmen a Pékin.
Dandalin Tiananmen a Pékin. 64memo.com

Hukumomi a kasar China sun tsaurara matakan tsaro a yau laraba, yayin da ake tunawa da cika shekaru 25 da barkewar zanga-zangar neman sauyi a dandalin Tiananmen.A ranar 4 ga watan Yunin shekarar 1989 ne dubban dalibai, ma’aikatan kwadago, malaman jami’o’i da kuma ‘yan jarida suka gudanar da taron gangami a wannan dandali da ke tsakiyar birnin Beijing, to sai dai jami’an tsaro sun yi amfani da karfi domin murkushe zanga-zangar. Yanzu haka dai akwai wasu kungiyoyi da ke ci gaba da gwagwarmaya domin samun karin ‘yanci a kasar ta China, kuma a halin yanzu akwai masu irin wannan gwagwarmaya akalla 30 da aka yi wa daurin talala, sannan wasu 17 ke daure a gidan yari.