Syria

Assad ya lashe zaben Syria

Magoya bayan Shugaban Syria Bashar al Assad
Magoya bayan Shugaban Syria Bashar al Assad REUTERS/Khaled al-Hariri

Bashar al Assad ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar Syria wanda ‘Yan adawa a kasar suka yi watsi da zaben. Assad ya lashe zaben ne da rinjaye kuri’u kashi 88.7, rata mai yawa tsakanin shi da abokan takarar shi guda biyu.

Talla

Kakakin Majalisar Syria Mohammed al-Lahham wanda ya bayyana sakamakon zaben yace Hassan al-Nuri ya samu kuri’u kashi 4.2, yayin da kuma Maher al-Hajjar ya samu kuri’u kashi 3.2.

A cikin jawabinsa na murnar lashe zaben, Shugaba Assad ya godewa mutanen Syria da suka zabe shi.

Amma ‘Yan tawayen kasar wadanda suka kauracewa zaben sun sha alwashin ci gaba da yaki da Assad har sai sun kawar da gwamnatinsa bayan sun shafe sama da shekaru 3 suna yaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.