Isra'ila

Isra’ila zata gina sabbin gidaje a yankunan Falesdinawa

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu REUTERS/Gali Tibbon

Kasar Isra’ila tace tana shirin gina sabbin gidaje 1,500, domin mayar da martani ga gwamnatin Falesdinawa da ta hada kawance da Hamas. Shugabannin Falesidinawa sun yi kira ga Amurka ta dauki mataki akan Isra’ila.

Talla

Isra’ila zata gina sabbin gidajen ne a yankunan Falesdinawa da ta mamaye a gabacin birnin Kudus da kuma yamma da kogin Jordan.

Ma’aikatar gidaje a kasar Isra’ila tace wannan martani ne akan kawancen da gwamnatin Falesdinawa ta kulla da Hamas, duk da kasashen yammaci da Amurka sun amince su yi aiki tare da sabuwar gwamnatin Hadin kan ta Falasdinawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.