Afghanistan

Ambaliyar ruwa ta yi ta’adi a Afghanistan

Yankin Badakhshan a Afghanistan
Yankin Badakhshan a Afghanistan AFP PHOTO/ ROBERTO SCHMIDT

Akalla mutane 73 aka ruwaito sun mutu a kasar Afghanistan sakamakon ambaliyar ruwa da aka samu a yankin Baglan. ‘Yan sandan kasar sun ce ambaliyar ta raba dubban mutane ne da gidajensu. cikin wadanda suka mutu akwai mata da yara kanana, yayin da kuma ‘Yan sandan kasar suka ce kimanin mutane 200 ne suka bata.