Iraqi

Mayakan Jihadi sun yi garkuwa da Jami’a a Iraq

Wasu jami'an tsaron kasar Iraqi
Wasu jami'an tsaron kasar Iraqi REUTERS/Stringer

Mayakan Jihadi a kasar Iraqi sun yi garkuwa da Dalibai da Malaman Jami’ar Anbar da ke cikin birnin Ramadi, yayin da mutane 59 suka mutu a musayar wuta da aka yi tsakanin ‘Yan bindigar da kuma Jami’an tsaro. ‘Yan sandan kasar sun ce ‘Yan bindigar sun abka ne a cikin Jami’ar tare da kashe masu gadi da kuma tarwatsa gadar da ke isa kofar shiga Makarantar.

Talla

Rahotanni sun ce Jami’an tsaron sun yi musayar wuta da ‘Yan bindigar domin kokarin kwato Jami’ar da suka karbe ikonta, lamarin da ya janyo hasarar rayuka da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.