Malaysia-China

Za a baiwa wanda ke da bayani kan jirgin Malaysia kyutar kudi

Masu aikin binciken jirgin saman Malaysia, da yayi batan dabo
Masu aikin binciken jirgin saman Malaysia, da yayi batan dabo Reuters/路透社

Yau Lahadi ‘Yan uwan Fasinjojin da ke cikin jirgin saman nan mallakin kasar Malaysia, daya yi batan dabo yau watannin 3, sun kaddamar da wani asusun da zai samar da kudi Dalar Amurka Miliyon 5, da za a baiwa duk wanda ya bayar da bayanai kan hakikanin abinda ya faru da jirgin. Ranar 8 ga watan Maris aka daina jin duriyar jirgin, daya taso da Kuala Lumpur a Malaysia zuwa birnin Beijing na China, dauke da mutanen 239, kuma kusan kashi 2 cikin 3n su ‘yan kasar China ne.Ana tunanin jirgin kirara 777 ya fada a kudancin tekun Indiya ne, amma rashin gano burbushinsa ya sa ‘yan uwan fasinjojnin ke zargin rufa rufa a lamarin.