Syria

Assad ya yi ahuwa ga wasu da ake tsare da su

Shugaba Bashar al- Assad na Syria
Shugaba Bashar al- Assad na Syria REUTERS/SANA/Handout via Reuters

Shugaban kasar Syria, Bashar al- Assad ya bayyana yin ahuwa ga ‘yan kasar da ake tsare da su kafin 9 ga watan Yuni wannan shekara, sakamakon nasarar zabe da ya samu a zaben shugabancin kasar da aka yi wanda ya lashe da gagarumin rinjaye.

Talla

Ministan sahria’r kasar, Najem al Ahmed, ya ce anyi ahuwar ne dan hada kan ‘yan kasar, yafewa juna da kuma bude wani sabon babi.

Zaben da aka wa Assad ya samu suka matuka daga kasashen yammacin duniya inda suka zargi shi da karkata akalar zaben don taimakawa kanshi.

Akalla mutane kusan 1,000 ake tsare da su a gidajen yari daban daban na kasar wadanda ake sa ran za su amfana da wannan ahuwa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.