Malaysia

Iyalan Fasinjan jirgin Malaysia sun fara karbar diyya

'Yan uwan  Fasinjan Jirgin Malaysia da ya bata
'Yan uwan Fasinjan Jirgin Malaysia da ya bata ©Reuters.

Kamfanin jirgin Malaysia ya fara biyan wani kaso na kudaden diyya Dala dubu hamsin ga iyalan fasinjojin da ke cikin jirgin da ya bata mai suna MH370 da yanzu tsawon watanni uku ana cigiyar jirgin. Ma’aikatar harakokin waje tace mutane shida daga Malaysia da wasu ‘iyalan fasinjan China suka fara karbar kudaden.

Talla

Kamfanin yace zai biya dukkanin iyalan Fasinjoji 239 da matuka jirgin kudaden diyya.

Akwai kwamiti da kamfanin ya nada domin tantance magada ko makusantan fasinjan da ke cikin  jirgin.

A ranar 8 ga watan Maris ne Jirgin na Malaysia ya bata a kan hanyarsa daga birnin Kuala Lumpur zuwa Beijing, kuma har yanzu ba a gano inda Jirgin ya fada, duk da binciken kwa-kwaf da aka gudanar a yankin Australia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.