Iraq

Dubban mutanen Iraqi zasu rungumi makamai

Daruruwan mutanen Iraki da suka shiga aikin Soja domin yakar Mayakan da suka karbe ikon Mosul da wasu biranen arewacin kasar
Daruruwan mutanen Iraki da suka shiga aikin Soja domin yakar Mayakan da suka karbe ikon Mosul da wasu biranen arewacin kasar Reuters/

Dubban mutanen kasar Iraqi, yawancinsu mabiya akidar Shi’a sun mika kai domin taimakawa gwamnatin kasar don yakar Mayaka Sunni da suka karbe ikon wasu yankunan kasar. Wannan kuma na zuwa ne a yayin da Amurka tace zata sake agazawa Iraki domin kawo karshen rikicin da ke neman raba kasar gida biyu.

Talla

Dubban mutanen kasar za su yi yaki ne da masu gwagwarmayar neman kafa kasar Musulunci a Iraqi, domin amsa kiran Firaminista Nuril Maliki wanda yace a shirye ya ke ya ba fararen hula makamai.

Akwai sansani da aka bude domin horar da dubban mutanen dubarun soja.

Yanzu haka Mayakan sun karbe ikon wasu birane a arewaci da kuma arewacin tsakiyar Iraqi, yayin da kuma yanzu suka doshi yankin kudanci zuwa babban birnin kasar.

Wakilin kamfanin Dillacin labaran Faransa yace dubban mutane ne suka kai kansu a basu makamai domin shiga yaki gadan gadan da mayakan na Jihadi. Wannan kuma ya biyo bayan kiran jagoran mabiya darikar Shi’a Ayatollah Ali al-Sistani, a hudubarsa a yau Juma’a.

Yanzu haka rahotanni sun ce akwai daruruwan mutane da suka kauracewa gidajensu a Biranen Tikrit da Samarra bayan Mayakan sun abka Biranen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.