Iran-Iraq

Iran zata taimakawa Iraqi

Shugaban kasar Iran, Hassan Rouhani
Shugaban kasar Iran, Hassan Rouhani پایگاه اطلاع رسانی ریاست جمهوری

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani yace Iran a shirye ta ke ta taimaki Iraqi wajen yaki da masu gwagwarmaya da suka karbe ikon wasu biranen arewacin kasar. Hakan ke nufin Iran zata yi aiki tare da Amurka a Iraqi wadanda da suka dade suna adawa da juna.

Talla

Tayin na Iran na zuwa ne bayan Sojojin Iraqi sun ce sun karbe ikon wasu biranen arewacin kasar guda biyu da Mayakan Sunni suka karbe iko.

Akwai dubban mutanen Iraqi da suka mika kai ga gwamnati domin taimakawa a fatattaki Mayakan.

Shugaba Rauhani ya musanta rahotannin da suka ce Iran ta aika da dakarun Soji zuwa Iraqi domin taimakawa Sojojin kasar.

Kungiyoyin Mayaka biyu ne ke yaki a Iraqi, wadanda yanzu suka nufi Bagadaza bayan sun karbe ikon Mosul da Tikrit.

Tuni Amurka ta sha alwashin zata agazawa Iraqi domin karya ‘Yan gwagwarmayar mabiya Sunni da ke neman ganin bayan gwamnatin Shi’a a Iraqi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.