Afghanistan

An kammala zabe a Afghanistan

Jami'an hukumar zaben a Afghanistan
Jami'an hukumar zaben a Afghanistan REUTERS/Omar Sobhani

Miliyoyan Mutanen kasar Afghanistan sun kada kuri’ar zaben shugaban kasa zagaye na biyu, duk da barazanar hare hare daga kungiyar Taliban. Yanzu haka an kammala jefa kuri’a, inda mutanen kasa suka zabi tsakanin Abdallah Abdullah da kuma Asharaf Ghani wadanda cikinsu wani zai gaji Hamid Karzai.

Talla

Duk da cewa an kammala zaben lami lafiya, amma a wasu yankunan kasar an kai wasu hare hare, ciki har da harin roka a kusa da wata runfar zabe a gabacin lardin Khost, inda aka samu hasarar rayukan mutane biyar.

Shugaban hukumar Zabe Ahmad Yusuf Nuristani ya yaba da yadda aka gudanar da zaben amma ya amsa cewa akwai inda aka samu matsalar karancin takardun kada kuri’a.

Wannan dai zai kasance karon farko da za’a samu sauyin gwamnati daga wata gwamnatin Dimokuradiya zuwa wata a tarihin Afghanistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.