Pakistan

An kashe Mayakan Taliban 80 a Pakistan

Hayaki ya turmuke tashar Jirgin sama a Karachi inda Mayakan Taliban suka kai wa hari a ranar Litinin
Hayaki ya turmuke tashar Jirgin sama a Karachi inda Mayakan Taliban suka kai wa hari a ranar Litinin REUTERS/Athar Hussain

Jiragen yakin kasar Pakistan sun kaddamar da hare hare a mabuyar Mayakan Taliban da ke addabar kasar a yankin arewa maso yammaci, inda Akalla mutane 80 suka mutu cikinsu har da Mayakan da ake zargin sun kai kazamin hari a tashar jirgin sama a Karachi.

Talla

Jami’an tsaro a arewacin Waziristan da aka kai harin ta sama sun ce Mayaka kimanin 150 ne aka kashe. Cikinsu kuma akwai mutane 38 da suka kai kazamin hari a ranar Litinin a tashar jirgin sama a Karachi.

An kai wa Mayakan harin ne a yankin Dehgan a arewacin Waziristan, inda nan ne mabuyar Mayakan Taliban da Al Qaeda da ke kusa da kan iyaka da Afghanistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.