Iraq

Sojojin Iraqi sun kashe Mayaka 279

Sojojin sa-kai da ke taimakawa dakarun Iraqi wajen yaki da Mayakan da suka karbe ikon biranen arewacin kasar.
Sojojin sa-kai da ke taimakawa dakarun Iraqi wajen yaki da Mayakan da suka karbe ikon biranen arewacin kasar. REUTERS/Alaa Al-Marjani

Jami’an tsaron kasar Iraqi sun kashe Mayaka ‘Yan gwagwarmaya kusan 300 bayan sun kaddamar da hare hare kan mayakan da suka karbe ikon wasu biranen arewacin kasar. Kakakin gwamnatin kasar Janar Qassem Atta yace mayaka 279 ne Sojojin kasar suka kashe cikin sa’o’I 24, tsakanin jiya Assabar zuwa yau Lahadi.

Talla

Tshohon mai shiga tsakanin rikicin Syria Lakhdar Brahimi yace rikicin Syria ne ya shafi Iraqi.

Yayin da kuma Jaridun Saudiya suka soki gwamnatin Shi’a ta Firaminista Nuril Maliki da haifar da rikicin da ya shafi Mayaka da ke bin akidar Sunni.

Rahotanni sun ce yanzu haka dakarun Gwamnatin Iraqi sun karbe ikon wasu biranen arewacin kasar guda biyu, amma har yanzu wasu biranen na karkashin ikon gungun kungiyoyin Mayaka guda uku da ke neman kawo karshen gwamnatin Shi’a a Iraqi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.