Iraqi-Amurka

Soji sun kashe masu tada Kayar baya kusan 300 a Iraqi

foxnews.com

Jami’an tsaron kasar Iraqi sun kashe masu tada Kayar baya kusan 300 bayan sun kaddamar da hare-hare kan mayakan, da suka karbe ikon wasu biranen arewacin kasar

Talla

Kakakin gwamnatin kasar Janar Qassem Atta ya ce mayaka 279 ne Sojojin Iraqi suka kashe cikin sa’o’I 24 wato tsakanin Assabar da Lahadi.
Tsohon mai shiga tsakanin rikicin Syria Lakhdar Brahimi yace rikicin Syria ne ya shafi Iraqi.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Jaridun kasar Saudiya suka soki gwamnatin Firaminista Nuril Maliki da haifar da rikicin da ya shafi Mayaka da ke bin akidar Sunni.
Rahotanni sun ce yanzu haka dakarun Gwamnatin Iraqi sun karbe ikon wasu biranen arewacin kasar guda biyu, amma har yanzu wasu biranen na karkashin ikon gungun kungiyoyin Mayaka guda uku da ke neman kawo karshen gwamnatin kasar ta Iraqi.

A halin da ake ciki kuma Ofishin jakadancin kasar Amurka a birnin Baghdada na can yana kwashe ma’aikatansa, tare da kara yawan Dakaru bayan da masu tada kayar baya suka kwace wasu yankuna, suna kuma kara matsawa zuwa babban birnin kasar.

Sai dai ba’a san yawan ma’aikatan da za’a washe daga Ofishin jakadancin Amurka ba a kasar, sai dai mai magana da yawun hukumar tsaro ta Amurka Jen Psaki ya ce kwashe ma’aikatan da wuccin gadi ne kuma ana kai su ne a birnin Basar.

Masu lura da al’amurra dai na ganin cewar kusan shekaru Ukku da Dakarun Amurka suka washe a Iraq basu yi wani tasiri ba, lura da yanda matsalar tsaro a kasar ke dada ruruwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.