India

MDD ta nemi India ta mayar da hankali kan hukunta masu aikata laifukan fyade

kwamishinan kare hakkin bil adama ta MDD, Navy Pillay
kwamishinan kare hakkin bil adama ta MDD, Navy Pillay REUTERS/Mohammad Ismail

Hukumar kare hakin dan adama ta Human right Watch a jiya talata ta shawarci kasar India da ta tabbatar da hukunta duk wadanda aka kama da aikata fyade domin shawo kan matsalar da yanzu haka ke zama barazana ga mata a kasar. 

Talla

Kwamishinan kare hakkin bil adama ta MDD, Navi Pillay ce ta yi wannan kira a wata ganawa ta bayan fage, yayin da majalisar ta ke wani taro.

“Matan dake suka fito daga bangaren al’umomin da ake kyamata, suna fama da matsaloli biyu, wadanda suka hada da kyamar launin fatarsu da kuma wariya ta bangaren jinsi.” In ji Pillay.

Hukumomi a kasar ta India, sun jima suna yaki da muzgunawa mata da ake yi a kasar, musamman ma ta hanyar fyade, lamarin da kasashen duniya suke ganin gazawar hukumomin kasar.

Ko a watan jiya, an yiwa wasu mata yara ‘yan shekaru 12 da 14 fyade, aka kuma kashe su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.