Iraqi-Amurka

Gwamnatin Amurka ta gargadi Iraqi kan mayar da rikicin kasar na addini

Wasu Sojan sa kai na kasar Iraqi, da ke tamakawa sojojin kasar yaki da 'yan tawaye
Wasu Sojan sa kai na kasar Iraqi, da ke tamakawa sojojin kasar yaki da 'yan tawaye Reuters/路透社

Jami’an gwamnatin Amurka sun gargadi Priministan Iraqi Nuri al-Maliki, kan mayar da rikicicin kasar na addini. Ana ci gaba da sukan Prime Ministan na a daidai lokacin da gwamnatin shi ke kokarin fatattakar ‘yan tawayen kasar, da suke ci gaba da karbar manyan biranen kasar, bayan da suka karba birnin Mosul a baya bayan nan.Tashe tashen hankulan da aka shafe kwanaki 9 ana yi a kasar ta Iraqi sun yi sanadiyar dubun dubatar ‘yan kasar barin gidajen su, yayin da wasu da dama suka rasa rayukansu, baya ga ‘yan kasashen Indiya da Tukiyya da aka sace.Sai dai mai Magana da yawun fadar gwamnatin Amurka ta White House Jay Carney yace gwanmatin alhakin kare rayukan jama’a na kan hgwamnatin kasar.Carney yace dole hukumomin Iraqi su tauki matakan kare kasar, yace Amurka ta shafe fiye da shekatru 8 a kasar, kuma ta kashe makudan kudade, don kawai a baiwa iraqi damar samun ci gaba a harkar Democradiyya, a matsayin ‘yantacciyar kasa. Yace kamata yayi hukumomin kasar su dauki matakai masu muhimmanci, wagen yin shugabanci ba tare da nuna banbacin addini ba.A halin da ake ciki kuma, Prime Ministan ya kuma nemi sojan kasar da suka yi ritaya, su dawo kagen fama don ganin an ceto kasar daga fadawa yakin basasa.Ita ma kasar Saudi Arabiya ta yi gargadin afkuwar yakin basasa a kasar ta Iraqi, tare da illar da hakan zai jawo a yankin gabas ta tsakiya.