Malaysia-Australia

An koma aikin neman jirgin Malaysia

Masu aikin nemen Jirgin Malaysia  MH370 da ya bata
Masu aikin nemen Jirgin Malaysia MH370 da ya bata AFP PHOTO / POOL / RICHARD WAINWRIGHT

Mahukuntan kasar Australia sun ce za’a koma aikin neman jirgin kasar Malaysia da ya bata a kudancin yankin da ake tunanin jirgin ya fadi sakamakon wasu sabbin bayanai da aka samu da ke nuna alamun hangen tarkacen jirgin.

Talla

Rahotanni sun ce masu aikin binciken jirgin zasu soma binciken ne a yamma da birnin Perth. Amma hukumar da ke kare aukurar hadari a Australia da ke jagorantar bincike ba ta bayyana inda aka hango tarkacen jirgin ba amma tace masu binciken za su doshi kudu.

Jirgin Malaysia ya bata ne a ranar 8 ga watan Maris akan hanyarsa daga Kuala Lumpur zuwa Beijing dauke da fasinja 234, yawancinsu mutanen kasar China.

Yanzu kamfanin jirgin na Malaysia ya fara biyan ‘Yan uwan fasinjan da ke cikin jirgin kudaden diyya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.