China

'Yan sandan China sun kashe mahara 13 a yammacin kasar

Shugaban kasar China Xi Jinping
Shugaban kasar China Xi Jinping Reuters/路透社

‘Yan sandan kasar China sun ce yau asabar sun kashe mutane 13 a lardin Xinjiang mai fama da tashe tashen hankula, lokacin da suka afka wani ofishin ‘yan sanda suka kuma tayar da bama bamai. Wani shafin internet na gwamnatin yankin, daya bayar da sanarwar harin, yace akwai ‘yan sandan da suka sami raunuka sakamakon harin, sai dai ba dan sandan daya mutu.Yankin na yammacin kasar, da akasarin mazauna musulmi ne ‘yan kabilar Uighur marasa rinjaye, ya yi ta fuskantar tashe tashen hankula a ‘yan shekarun nan.