Pakistan

An yi wa wata Mata fyade tare da rataye ta a Pakistan

Itaciyar da aka rataye wata Yarinya a kasar Indiya bayan an yi mata Fyade.
Itaciyar da aka rataye wata Yarinya a kasar Indiya bayan an yi mata Fyade. AFP

Wasu gungun Maza sun yi wa wata yarinya fyade mai shekaru 21 tare da rataye ta a itaciya a yankin Punjab a kasar Pakistan. Irin wannan al’amari ne ya janyo bore a kasar India da ke makawabtaka da Pakistan. ‘Yanzu haka saurayin yarinyar mai suna Muhammaad Saqib yana hannun ‘Yan sanda wanda ya amsa shi ne ya jogaranci yin fyden.

Talla

‘Yan sandan Pakistan sun ce abokan saurayin ne suka yi wa Yarinyar fayde bayan ta ki amincewa da bukatar saurayin akan ta bari su kwanta da ita.

Bayan sun yi mata fayde ne aka tsince gawarta a rataye a itaciya, da nufin fakewa akan ta kashe kanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.