Amurka-Iraqi

Amurka na kokarin sasanta rikicin kasar Iraqi

REUTERS/Jacquelyn Martin/Pool

Yau Lahadi, Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya nufi yankin gabas ta tsakiya, a wani kokarin da yake yin a sasanta rikicin daya barke a kasar Iraqi.‘Yan tawaye kasar, mabiya sunni sun karbe wasu yankunan arewaci, a wani tawayen da ake gani zai iya sanadiyyar rarrabuwar kanun ‘yan kasar ta bangaren addini.Sai dai suma mayaka ‘yan shi’a suna ci gaba da tallafa wa sojan gwamnati, don ganin an fatattaki ‘yan tawayen.Tuni kasar Iran ta yi tayin baiwa hukumomin birnin Bagadaza tallafi don ganin an fatattaki ‘yan tawayen.Gwamnatin Iraqi karkashin Prime Minister Nouri al-Maliki ta mabiya Shi’ah ce, yayin da ‘yan tawayen kuma akasarinsu magoya bayar hambararren shugaba marigayi Saddan Husaine ne.