Isra'ila-Falesdinawa

Isra'ila ta kashe Palasdinawa 2 ta kame 10

Prime Ministan Isra'ila, Benyamin Netanyahu
Prime Ministan Isra'ila, Benyamin Netanyahu REUTERS/Larry Downing

Yau Lahadi, dakarun kasar Isara’ila sun ce sun kashe wasu matasan Palasdinwa 2, a lakacin wani fadan da aka yi a yammacin kogin Jordan. Tun a jiya Asabar suka sake kama wasu Palasdinawa 10 a yankin, yayin da sojojin ke ci gaba da matsa kaimi wajen neman wasu matasa 3 da ake ganin sace su aka yi.Sojan sun ce zuwa yanzu sun kama Palesdinwa 340, kuma 240 daga ciki ‘yan kugiyar Hamas ne.Isra’ila na zargin kungiyar ta Hamas da sace matasan, masu shekru 16 su 2, da dan shekaru 19 guda daya.