Iraq

Mayakan Iraqi sun sake karbe ikon wasu birane

Mayakan kasar Iraqi da suka karbe ikon wasu biranen kasar
Mayakan kasar Iraqi da suka karbe ikon wasu biranen kasar

Masu gwagwarmaya a kasar Iraqi sun sake karbe ikon wasu biranen yammacin kasar, a yayin da Sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry ya isa yankin domin shawo kan rikicin kasar. Mayakan da ke gwagwarmayar kawo karshen gwamnatin Shi’a a Iraqi sun karbe ikon biranen Rawa da Ana bayan sun karbe ikon Al Qaim kan iyaka da Syria a jiya Lahadi.

Talla

Rahotanni sun ce dakarun gwamnatin Iraqi sun fice daga biranen da suka fada ikon Mayakan masu neman shinfida sabuwar daular Islama a Iraqi.

Kasar Amurka dai na nazarin yadda zata taimakawa kasar Iraqi a rikicin kasar da shugaba Obama ke yi wa kallon na Siyasa da banbancin akida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.