Korea ta Kudu

Sojan Korea ya bindige Sojoji 5

Shugabar kasar Koriya ta Kudu Park Geun-hye tana zubar da hawaye bayan wani jirgi ya kife da mutanen kasar a teku
Shugabar kasar Koriya ta Kudu Park Geun-hye tana zubar da hawaye bayan wani jirgi ya kife da mutanen kasar a teku Reuters

Dubban Sojojin kasar Korea ta Kudu da ‘Yan sanda suka shiga farautar wani Soja da ya bindige wasu Sojoji guda biyar har lahira a cikin darern jiya Assabar. Akwai kuma wasu mutane bakwai da Sojan ya bari rai ga hannun Allah bayan ya bude wa abokan aikinsa wuta da ke bataliya ta 22 a lardin yammacin Gangwon.

Talla

Kakakin rundunar Sojin Korea ta kudu yace an tursasawa Sojan ne shiga aikin Soja, kuma ya tsere ne dauke da makamai da bindiga kirar k2 da ya bindige Sojojin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.