Syria

Isra’ela ta kashe Sojin Siriya 10 a wani harin tsakkiyar Dare, ta Sama

timesofisrael.com

Akalla Sojin kasar Siriya 10 ne aka kashe yayin da kasar Isra’ela ta kai hari ta Sama a cikin tsakkiyar Daren jiya Lahadi a cikin kasar ta Siriya inda ‘yan tawaye ke ci gaba da fada da Dakarun gwamnatin shugaba Bashar al-assad

Talla

Harin dai ya auku ne a kusa da kan iyakokin kasashen biyu a wani yanki da kasar Israela ke rike da shi na Golan Heights, kamar yanda wata kungiya mai sa Ido kan abubuwan da ke wakana a kasar ta tabbatar.

Akalla dai Makamai masu linzami 9 ne Israela ta harbawa sojin kasar Siriya ta hanyar amfani da wani Jirgin sama, inda suka lalata Tankokin yaki 2 da Makaman Artillery 2.

Harin haka ma ya hallaka wani Matashi Balarabe dan dan wani dan kwangilar ma’aikatar tsaron kasar Israela a yankin Golan lokacin da aka kai harin yana tafiya a yankin tare da Mahaifinsa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.