Iraqi-Amurka

Mayakan Sunni sun kwace wasu yankunan kasar Iraqi

nydailynews.com

Rahotanni daga kasar Iraqi, na cewa mayakan Sunni sun kutsa kai a yammacin kasar, bayan da suka karbe wani muhimmin wuri da ke kan iyakar Iraqi da Syria. Wannan kuma na faruwa ne a dai dai lokacin da bayannai ke nuna cewa mayakan sun kashe mutane da dama a wasu garuruwa guda biyu.

Talla

Karbe yankunan da mayakan na Sunni suka yi, ya tilastawa Dakarun Iraqi janyewa daga yankunan, matakin da gwamnatin kasar ta bayyana a matsayin wata dabarar Yaki.

Wannan aranmaga da ake yi, na samun jagorancin kungiyar ISIL ta masu tada kayar baya a tsakanin kasar ta Iraqi da Syria, wacce kuma kungiya ce da ke taimakawa ‘yan tawayen Syria wajen yakar shugaba Bashar al-Assad.

Yanzu haka hukumomi a Washington na kasar Amurka na nuna matsin lamba, ga kasashen larabawa da su matsantawa hukumomin Iraqi lamba kan su gaggauta kafa gwamnati.

Wannan dai na faruwa ne a dai dai lokacin da bayanai ke nuna cewa mayakan na Sunni, sun kashe akalla mutane 21 a garuruwan Rawa da Ana, jim kadan bayan da Dakarun Iraqi suka janye a wadannan garuruwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.