Pakistan

An yi arangama tsakanin ‘yan sandan Pakistan da magoya bayan wani malamin addini

Wasu jami'an tsaron kasar Pakistan
Wasu jami'an tsaron kasar Pakistan

A Pakistan Malamin addinin nan Tahir-ul-qadri dake gwagwarmayar ganin ya dawo kasar daga Canada domin gudanar da wani taron gangami na neman kawo sauyi a mulkin kasar, ya yi sanadiyar barkewar wata arangama tsakanin magoya bayansa da ‘yan sanda.

Talla

A watan Janairun da ya gabata ne dai shehin malamin ya umarci dubban magoya bayansa da gudanar da zaman dirshan a gidajensu, domin nuna adawa da gwamnatin kasar

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da ake dakon isowar Qadri, inda wani fada ya barke tsakanin magoya bayansa da jami’an tsaro, lamarin da bayanai suka tabbatar da jikkatar ‘yansanda 70

Wannan na zuwa ne dai a daidai lokacin da Fira ministan kasar Nawaz Sharrif ke fama da matsin lamba a sha’anin tsaron kasar ta Pakistan.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.