India

Bene ya rubta da mutane da dama a India

Masu aikin Ceto suna kokarin kubutar da mutunen da suka makale a cikin benen da ya rubta a yankin Tamil Nadu a India
Masu aikin Ceto suna kokarin kubutar da mutunen da suka makale a cikin benen da ya rubta a yankin Tamil Nadu a India REUTERS/Babu

Akalla mutane 11 aka ruwaito sun mutu, sakamakon rubtawar wani bene hawa 11 saboda ruwan sama da aka tabka a kudancin India . Masu aikin ceto yanzu haka suna kokarin ceto rayukan mutane da dama da suka makale a cikin benen. Benen ya rushe ne a jiya Assabar bayan an samu mutuwar mutane 10 sakamakon rushewar wani gida a birnin New Delhi.

Talla

Wani Jami’in ‘Yan sanda ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa cewa gawawwakin mutane 11 ne aka fitar daga cikin benen da ya rushe a Jahar Tamil Nadu, kuma an yi nasarar ceto mutane 20.

‘Yan sanda kuma sun cafke wanda ke da mallakin benen da kuma injiniyoyin da suka gina benen.

Gwamnatin Jahar Tamil Nadu tace zata biya diyyar kudi da suka kai dala dubu uku ga ‘Yan uwan wadanda suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.