Koriya ta Kudu-Koriya ta Arewa

Koriya ta Arewa ta sake harba makami mai linzami a kan teku

Shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong Un
Shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong Un Reuters/路透社

Yayin da shugaban kasar China Xi Jinping ke shirin kai ziyara Koriya ta Kudu, yau Lahadi Koriya ta Arewa ta sake harba wasu makamai amsu linzami samfurin Scud, a kan tekun kasashen. Dama a ranar Alhamis data gabata hukumomin na birnin Pyongyang suka harba wasu makaman masu linzami 3.Ana sa rai shugaban na China, kasar da keda alaka ta kut da kut da hukumomin Pyongyang, zai tattauna batun Nukiliyan kasar Koriya ta Arewan, yayin ziyara da zai fara a ranar Alhamis mai zuwa.