India

An ciro gawarwakin mutane daga ginin da ya rushe a India

Masu aikin ceto suna kokarin kubutar da mutunen da suka makale a cikin benen da ya rubta a yankin Tamil Nadu a India
Masu aikin ceto suna kokarin kubutar da mutunen da suka makale a cikin benen da ya rubta a yankin Tamil Nadu a India REUTERS/Babu

Masu aikin ceto a kasar Indiya, sun gano wasu gawarwaki a karkashin tarkacen wani gini da ya rufta ranar asabar da ta gabata. Izuwa yanzu yawan wadanda suka rasa rayukansu a wannan lamari ya kai mutane 18.

Talla

Wani babban jami’in ‘yan sanda a jihar Tamil Nadu inda lamarin ya faru mai suna Karuna Sagar, ya ce yanzu haka suna rike da mutane shida cikinsu kuwa har da wanda ya mallaki gidan, da dansa, bisa zargin sakaci.

Rahotanni sun ce masu ayyukan ceto sun yi amfani ne da mashina masu hako kasa da  kayayyakin yanke yanke ne wajen neman sauran mutanen da lamarin ya rutsa da su.
Har yanzu babu takaimaiman yawan mutanen da ba a gansu ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.