Iraq

'Yan tawaye sun yi ikirarin kafa daular musulunci a Iraki

Abu Bakr Bagdadi, shugaban ISIL a Iraki
Abu Bakr Bagdadi, shugaban ISIL a Iraki

‘Yan tawaye da ke ci gaba da gwabza fada da dakarun gwamnatin kasar Iraki, sun sanar da kafa daular musulunci a kasar tare da bayyana shugabansu Abu Bakr al-Baghdadi a matsayin Khalifa kuma jagora.

Talla

A wata sanarwa da suka fitar a ranar lahadi, ’yan tawayen sun bayyana cewa sabuwar daular musuluncin da suka kafa ba wai ta takaita ne a cikin kasar Iraki kawai ba, domin kuwa ta hada dukkanin kasashen yankin, tare da yin kira ga al’umma da su yi wa sabon jagoran mubaya’a.

Shi dai wannan mataki da mayaka ‘yan Sunni suka dauka, na a matsayin kalubale ga kungiyar Alqa’ida wadda ta jima tana kiran kanta kungiya daya da ke neman kafa daular musulunci a yanki da kuma sauran kasashen duniya.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da mabiya mazhabar Shi’a a kasar ta Iraki ke ci gaba da kafa rundunonin mayakan sa-kai domin fuskantar ‘yan tawayen da dukkaninsu ‘yan Sunni ne.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.