Isra'ila-Falesdinawa

Isra'ila ta kaddamar da yaki kan zirin Gaza

Wasu hare-haren Isra'ila kan mashigin Rafah na yankin Gaza
Wasu hare-haren Isra'ila kan mashigin Rafah na yankin Gaza REUTERS/Abed Rahim Khatib

Jiragen yakin Isra’ila sun share tsawon daren jiya ruwan bama-bamai a kan yankin Gaza, a wani mataki da Isra’ilan ta kira na ‘’kare kai’’ daga hare-haren da Palasdinawa ke kai mata daga yankin na Gaza.

Talla

Majiyoyi daga yankin na Gaza sun ce sojan saman na Isra’ial sun kai hare-hare fiye da 30 a cikin daren litinin zuwa wayewar garin talata, to sai dai kawo yanzu babu cikakken alkalumma dangane da yawan mutanen da suka rasa rayukansu a lamarin.

A nata bangare Isra’ila ta ce Yahudawa biyu ne suka samu raunuka a jiya litinin, sakamakon fadawar rokoki Hamas a cikin yankunanta.

Rikici ya sake barkewa ne tsakanin Isra’ila da kuma Hamas da ke rikke da madafan ikon Gaza bayan da aka tsinci gawarwakin wasu matasan Yahudawa 3 da aka Falasdinawa ne suka sace su a kusa da yankin na Gaza, yayin da su kuma Yahudawa suka kashe wani matashin Bafalasdine a matsayin daukar fansa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.