Ira'ila

Sakataren Majalisar dunkin Duniya yace Isra'ila ta kashe Falesdinawa fiye da 172

Kasar Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare ta Sama da Makaman Artillery a yankin Zirin Gaza duk da kiraye-kirayen da hukumomin kasa-da-kasa ke yi mata na ta dakatar da kisan Palesdinawa Musulmi masu Azumi a Baki

Talla

Shaidun gani da Ido dai sun bayyana cewar hare-haren da Isra’ila ta kai da Jiragen yaki cikin Daren jiya sun lalata wani sashe na atisayen Dakarun Kungiyar Hamas da na Ezzudeen al-Qasm, amma babu ko mutum daya da ta kashe.

Haka ma hare-haren sun doki wani Gini da ake kira Darul-Balah da ke a cikin yankin Zirin Gaza, da wani yanki na Arewacin garin Jabaliyya.

A wannan harin dai an ce wasu mutane sun dan jikkata, haka ma akwai wani ruwan Wuta da Isra’ilar ta yi a Baitil Lahiyah a yankin Arewacin Zirin Gaza inda dama Isra’ila ta yi kashediun cewar za ta kai harin a can.

Sakataren Majalisar dunkin Duniya Ban ki moon ya bayyana cewar ya zuwa yanzu Isra’ila ta kashe akalla Falesdinawa 172 wasu 1,230 kuma suka jikkata.

Ban ki moon kuma ya yi kira akan Isra’ila da ta ji tsoron Allah akan kisan bayinsa, a yayin da a nata haujin, Isra’ila bata da wani alamun barin kai harin ga al’ummar Musulmin Falesdinu masu azumi a Baki.

Duk da ire-iren wadannan hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Falesdinawan, su kuma cewa suke, basu ta jin rashin tsoron Isra’ila ba a Duniya irin yanzu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.