Isra'ila-Falesdinawa

Isra'ila ta sake kaddamar da yaki kan zirin Gaza

Hare haren Isra'ila a yankin Gaza
Hare haren Isra'ila a yankin Gaza REUTERS/Baz Ratner

Kasar Isra’ila ta umurci dubban Falasdinawa da su fice daga gidajen su dake Arewaci da Gabashin Gaza zuwa yau da safe yayin da ta ci gaba da kai hare hare yankin bayan karyewar yarjejeniyar tsagaita wuta.

Talla

Firaminista Benjamin Netanyahu ya ce tunda an kasa samun tsagaita wuta to amsar su itace ci gaba da ruwan wuta, yayi da Kungiyar Hamas ta sa kafa ta yi fatali da tayin tsagaita buda wuta tsakanin ta da Isra’ila da kasar Masar ta gabatar,
Yarjejeniyar da ya kamata a ce ta fara aiki tun safiyar jiya talata.

Alkaluman mamata yanzu haka dai sun kai 192, a wata daya da Israela tayi tana aman wuta a yankin Gaza.

A nata bangaren Kungiyar Hamsa wadda ta chilla rokoki akalla dubu daya, tace babu batun sulhu muddin dai ba za a kulla yarjejeniya  warware dukkan batutuwan da ake takaddama a kai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.