Isra'ila-Falesdinawa

Majalisar dunkin Duniya ta damu da yawan Rayukan da Isra’ila ke kashewa a Gaza

davidduke.com

Kwamitin tsaro na MDD ya sake yin kiran tsagaita buda wuta a birnin Gaza tare da bayyana matukar damuwarsa kan yawan hasarar rayukan da ake ci gaba da samu

Talla

Yanzu haka dai an rasa Rayuka sama da 500 tun farkon somawar rikicin, a yayinda ranar jiya lahadi ta zama ranar da rayukan Falasdinawa suka fi salwanta a hare-haren da Isra’ilar ke ci gaba da kai masu.

Kwana guda bayan bayan ranar ta jiya lahadi da Rayukan falasdinawa suka fi salwanta tun farkon somawar hare haren da Isra’ila ke kai masu a birnin Gaza inda aka bayyana cewa falesdinawa 120 sun rasa rayukansu wasu daruruwa kuma sun jikkata, a yayinda Isra’ilar kuma ta yi hasarar sojojinta 13, Kasashe 15 mambobin kwamitin tsaro na Majalisar ta dunkin Duniya, sun bukaci Isra’ila da ta mutunta dokokin jinkai na Duniya musaman ta wajen kare rayukan fararen hula.

Kwamitin tsaron dai ya fadi haka ne a cikin wata sanarwar day a fitar bayan kwashe tsawon Sa’o’i 2 yana tattaunawa kan halin da ake ciki a birnin Gaza.

A jiya dai Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya jinjinawa manyan kasashen Duniya kan irin goyon bayan da suke baiwa kasarsa kan hare-haren da ta ke kaiwa Falesdinawan, inda ya kara da cewa kasarsa za ta yi duk abinda ya dace domin kare kanta daga hare-haren da kungiyar Hamas ke kai masu.

Yanzu haka dai wayewar safiya kawo yanzu an gano gawawakin Falesdinawa 16 wadanda suka hada da kananan yara 7 a cikin buraguzan wani gida da ya rushe a Khan Yunes, da ke a yankin kudancin Gaza, al’amarin da ya sa yawan Falesdinawan da hare-haren na Isra’ila suka kashe kaiwa ga 501 tun farkon rikicin kasa da makwanni 2 da suka gabata.

Kungiyar Hamas dai a bayan nan ta bayyana kama wasu Sojin Isra’ila da Kungiyar ta ce yanzu haka suna a Hannu, amma kasar ta Isra’ila, ta musanta wannan labarin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.