Amurka-Isra'ila

Hare haren da Isra'ila ta kai sun yi sanadiyyar mutuwar Falasdinwa fiye da 100

Hayaki na tsai a wuraren da Isra'ila ke kai hari a yankunan Falasdinawa
Hayaki na tsai a wuraren da Isra'ila ke kai hari a yankunan Falasdinawa Reuters/路透社

A kalla Falasdinwa 107 ne suka mutu, wani sojan Is’irala kuma ya bace, bayan da aka gagara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin kasar ta Yahudu da kungiyar Hamas. Isra’ilan ta ci gaba da kai hari ta sama, a yankunan Falasdinawa cikin dare jiya Juma’a, lamarin daya yi sanadiyyar mutuwar Pasdinawa 35 a garin Rafah kawai.Shugaban Amurka Barak Obama ya nemi a gaggauta sako sojan daya bace, da kuma ake gani gani ‘yasn kungiyar Hamas ne suka kama shi.A halin da ake ciki kuma, majalisun dokokin Amurka sun amince kasar ta bayar da kudin dalar miliyon 225, don tallafawa Isar’ila ta sayo makaman Karen harin makami mai linzami da kungiyar palasdiwa ta Hamas ke harba mata.Majalisar dattijai ce ta fara Amincewa da kudurin dokar bayar da tallafin, kafin daga bisan majalisa wakilai ma ta bi sawu, kuma wanna zai kara yawan gibin kasafin kudin Amurkan.Yanzu dokar na jiran amincewa shugaba Barak Obama ne, kafin ta fara aiki.