Lebanon

An yi musayar wuta tsakanin sojan kasar Lebanon da wasu 'yan bindiga

Prime Minister kasar Lebanon Tammam Salam
Prime Minister kasar Lebanon Tammam Salam AFP PHOTO / ANWAR AMRO

Sojojin kasar Lebanon 8 sun mutu a wani fito na fito da suka yi da ‘yan bindiga a gabashin kasar, kusa da kan iyakar kasar Syria. Rikicin ya taso ne bayan da aka kama, aka kuma tsare wani mutum da ake zargi da kungiyar mayakan jihadi ne.Cikin wata sanarwar da ta fitar, rundunar sojan kasar ta ce har zuwa wayewar garin yau Lahadi an ci gaba da fafatawar da ‘yan bindigar, kuma wasu sojojin sun sami raunuka.Rundunar tace tana tunkarar mayakan ne don kaucewa fantsamar rikincin kasar ta Syria zuwa lebanon.