Iran

Mutane 39 sun rasu a hatsarin jirgin saman Iran

Jirgin Iran da ya fado ranar 10 ga watan Agustan 2014 a Tehran
Jirgin Iran da ya fado ranar 10 ga watan Agustan 2014 a Tehran AFP PHOTO / ATTA KENARE

Hukumomi a kasar Iran sun tabbatar da mutuwar mutune 39 yayin da wasu 9 suka samu raunuka sakamakon hatsarin jirgin sama a birnin Tehran a ranar lahdin da ta gabata.

Talla

Jirgin saman kirar Antonov 140, ya rikito ne jim kadan bayan tashinsa daga filin sauka da tashin jiragen sama na Mehrabad da ke cikin birnin Tehran.

Shaidu sun ce jirgin ya fado ne a wani wuri mai tazarar mita 500 daga wata kasuwa. Ana dai samun yawaitar hatsurran jiragen sama a kasar ta Iran sakamakon tsufan jiragen sama sannan kuma kasar ke karkashin takunkuman kasashen duniya da ke haramta sayar ma ta da jiragen ko kuma kayayyakin gyaransu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI